A Yanzu Burina kawai Shi Ne Na Samu Miji Na Yi Aure - inji Teema Makamashi
Fitacciyar jaruma Fatima Muhammad Isah Yola
wadda aka fi sani da Teemah Makamashi, ta bayyana
muradin ta na samun miji Wanda hakan zai ba ta
dama ita ma ta je ta huta bayan gwagwarmayar da ta
sha a harkar fim, kafin Allah ya daga ta ta zama
babbar jarumar da a yanzu ake ji da ita a
masana'antar finafinai ta kannywood.
Teemah Makamashi ta bayyana hakan ne a lokacin
tattaunawar su da wakilin mu a game da irin nasarorin
da ta samu a matsayin ta na babbar jaruma, in da ta
fara da cewar " Kafin na samu daukaka duniya tasanni
na sha gwagwarmaya sosai a cikin masana'antar fim ,
amma a yanzu abin ya zama tarihi sai dai godiya ga
Allah musamman idan na kalli irin dunbun nasarorin
da na samu wannan kuma abin alfahari ne a gare ni.
Mun kuma tambaye ta game da kallon ta da ake yi a
matsayin jaruma mai aji Wanda hakan ya sa ake
shayin ta idan za a kira ta aikin fim sai ta ce " To ai aji
daban Sana'a daban, kuma mutunci ne ya ke jawowa
mutum haka.
domin na mutunta kaina ne ya sa ake shakka ta don
na san na gaba da ni , duk Wanda yake dama da ni
zan ba shi matsayin sa , idan kana sa'a na zan ba ka
matsayin ka , ina ganin hakan ne ya sa ake ganina a
matsayin mai aji.
Daga karshe ta bayyana mana burin ta in da take
cewa " A yanzu buri na shi ne na samu miji na yi aure
nima na je na huta a gidan miji na don haka ina
rokon Allah ya kawo mini miji nagari.
Mun Dauko Daga Shafin Arewasuper







